Falalu Dorayi tare da diyar shi Ummie

Babban direktan ya gargadi iyayen da su zamanto nagari kuma dinga yi ma yaran su addua

Idan da akwai abun da ya sanya fuskar ka/ki ya canja yanayi bisa ga wani bacin rai ko kana neman abun da zai debe maka kewa, wannan hoton Jarumin Kannywood da diyar shi zai taimaka.

Babban jarumi kuma mai bada umarni na fina-finai hausa Falalu Dorayi ya wallafa hoton shi tare da diyar shi a shafin sa na instagram.

"Ku kasance iyaye managarta, kuyi ma yaran ku addu'o'i.

Allah yayi miki albarka Ummie. Macen da ta haifi diya mace haihuwarta na farko tana tare da sa'a". Ya rubuta a shafin sa.

Allah shi raya. Ameen



source http://www.pulse.ng/hausa/hoton-falalu-dorayi-da-diyar-shi-mai-farantar-da-rai-id7880165.html
Share To:

Anonymous

Post A Comment:

0 comments so far,add yours