Shugaba buhari tare da Cif Olusegun Obasanjo a taron AU

Cikin bidiyon dake yawo a kafafen yada labarai za'a gan inda jiga-jigan ke wasa da dariya har ma tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya ari bakin yarbawa inda yake cewa "kilode nau''

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya hadu da shugaban kasa a taron majalisar kasashen afrika da aka gabatar a  kasar Habasha.

Cikin bidiyon dake yawo a kafafen yada labarai za'a gan inda jiga-jigan ke wasa da dariya har ma tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya ari bakin yarbawa inda yake cewa "kilode nau'' .

 

*Ministan Buhari na kulle-kulle wajen ganin an tsige Bukola Saraki daga mukamin shi - Inji Sanata

Tsabanin yanda wasu jama'a ke tsammani bayan wasikar da tsohon shugaban ya fitar wanda ya soki gwamnatin Buhari, jiga-jigan sunyi magana har da dariya haduwar su a taron.

Shima tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya halarci taron wanda aka gudanar a garin Addis Ababa a makon da ya gabata.

*Abubuwa  da ya kamata ka sani game da sabon shugaban hukumar NIA da Shugaban kasa ya nada

Wasikar Obasanjo

A wasikar da Obasanjo ya fitar yayi kira ga shugaba Buhari da kada ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019 kana ya kuma tuhumi Buhari da kasa farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma nuna fifiko ga wasu na kusa da shi.

Tsohon shugaban kasa wanda yayi mulki tsakani 1999 zuwa 2007 ya shawarci shugaba Buhari da ya zamanto mai bayar da shawara a harkar shugabancin kasar nan gaba domin yin haka zai fi muhimmanci a kasar dama sauran kasashen duniya.



source http://www.pulse.ng/hausa/buhari-da-obasanjo-sun-hadu-a-taron-au-id7906736.html
Share To:

Anonymous

Post A Comment:

0 comments so far,add yours