Funky Mallam tare da sabuwar amaryar shi

Wannan shine karo na biyu da dan wasan zai kara aure bayan mutuwar auren shi da tsohuwar matar shi Aisha.

Fitaccen dan wasan kwaikwayo Saheed Kabir wanda aka fi sani da Funky malam ya sake aure.

An daura auren shi da sabuwar amaryar shi a ranar asabar 27 ga wata 2018.

*Hotunan bikin fitaccen mawaki da amarya shi

Manyan baki da suka halarcin bikin auren shi sun hada da jakadar kamfanin Glo Sani Danja da Umar M.Shereef da sanannen mai tsara nauyukan kayan sawa na zamani Yusuf Guyson.

Mutuwar auren shi na farko

Wannan shine karo na biyu da dan wasan zai kara aure bayan mutuwar auren shi da tsohuwar matar shi Aisha.

*Babu wata salon mugunta da ban iya ba kuma da aure na nake yin fim- cewar Saratu Daso

A bayanin da ya fitar hirar shi da jaridar Vanguard kwanan baya, jarumin wanda ya kammala karatun sa a jami'ar Bayero dake kano ya shaida cewa ya rabu da tsohuwar matar shi da sharadi na cewa ba zai amshe ta idan ta nemi ta dawo bayan ta yunkura wajen ganin a raba auren su.

Auren shi da tsohuwar matar shi ya mutu bisa sabani da suka samu yayin da jarumin ke fuskantar karancin tattalin arziki

Auren shi da tsohuwar matar shi an samu albarkar da guda.



source http://www.pulse.ng/hausa/funky-mallam-ya-sake-aure-id7906378.html
Share To:

Anonymous

Post A Comment:

0 comments so far,add yours