Kungiyar yan wasan kwaikwayo ta jinjina ma gwamnan bisa matakin da ya dauka na daga dakatarwar da aka yi ma Rahama Sadau
Kungiyar yan wasan kwaikwayo na jihar kano ta jinjina ma gwamnan jihar Alhaji Abdullahi Umar Ganduje bisa daga dakatarwar da kungiyar masu shirya fina-finai tayi ma jaruma Rahama Sadau.
Shugaban kungiyar Alhaji Alhassan Kwalli yana mai cewa wannan matakin yana da amfani matuka a daidai wannan lokaci da masana'antar fina-finai hausa ke kokari wajen samad da cigaba a kasar ta hanyar ayukan ta.
A cikin takardar wanda mataimakin sakataren kungiyar Rabiu Rikadawa ya fitar ranar litinin, yayi ma gwamnan godiya kan daga dakatarwar da aka yi ma Rahama Sadau.
MOPPAN ta dakatar da Rahama bisa fitowar da tayi a cikin bidiyon mawaki Classiq wanda ya saba wa kai'idar kungiyar.
Ya kara jinjina ma mai girma gwamna bisa goyon baya da yake baiwa masana'antar fina-finan hausa da ma jaruman cikin ta.
*Dakatarwa da aka yi mun ya bude mun kofofin samun nasara
Shugaban yana mai la'akari cewa yan arewa nada labaruruka da al'adu da zata yada ma duniya kuma babban hanyar da za'a bi wajen yadda ta shine ta hanyar yin fina-finai masu kayatarwa da ilmantarwa.
Matakin da hukumar tace fina-finai ta dauka
A kwanan baya Rahama ta nemi gafarar duk wanda abubuwan da ta aikata a baya ya shafa tare da tura sakon neman gafara ga kungiyar MOPPAN.
Bayan hakurin da ta bayar da abubuwan da ta aikata wannan yayi sanadiya har aka kore ta daga harkar fina-finai Kannywood, a makon da ya gabata shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano Alhaji Ismail Naabba Afakallahu ya sanar cewa an yafe ma jarumar.
Afakallhu ya kara da cewa za'a cigaba da lura da shirye-shiryen fim da ta fito a ciki har ma da wadanda ta shirya da kanta.
Martanin MOPPAN
Bisa wannan matakin da hukumar tace fina-finai ta dauka na yafe ma jarumar, shugaban kungiyar MOPPAN Alhaji Kabiru Maikaba ya nuna rashin jituwa da matakin domin ba hukumar tace fina-finai ta dakatar da ita don haka Afakallahu ya daina masu shishigi cikin harkokin kungiyar su.
*Jaruman masana'antar Kannywood 6 da suka yi tasiri cikin 2017
Shugaban MOPPAN yace kungiyar bata yarda a dawo da ita cikin harkar fina-finai hausa har sai bayan ta dawo daga kasar Cyprus inda take karatu a halin yanzu.
A cewar Alhaji Kabiru Maikaba kungiyar tana jiran tattaunawa da jarumar domin ta wanke kanta daga abubuwan da ta aikata kana kungiyar zata san matakin da zata dauka a kan ta.
Wannan lamarin ya janyo cece-kuce tsakanin masu ruwa da tsaki na harkar fim har ma da masu bibiyan fina-finai hausa.
source http://ift.tt/2FJmdwu
Post A Comment:
0 comments so far,add yours