Masu garkuwan sun sace shi cikin watan disamba na bara kuma sun bukaci iyalin shi da biyan N75M a matsayin kudin fansar sakin shi
Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki na jihar Taraba Honorable Kosea Ibi sun kashe shi bayan kwanan 14 da sace shi.
A labarin da gidan telebijin ta Channels ta fitar al'ummar jihar Taraba na jimamin mutuwar dan majalisar.
An gano gawar dan majalisar mai wakiltar yankin Takum na jihar wanda yan bindiga suka sace ranar 30 ga watan Disamba na bara bayan sati biyu da yin haka.
Rundunar yan sanda na jihar ta tabbatar da mutuwar dan majlisar. Kakakin rundunar David Misal ya tabbatar ma manema labarai haka ranar 15 ga wata a Jalingo babban birnin jihar Taraba.
Misal yace an gano gawar Hosea Ibi a karamar hukumar Takum kuma yana sa ran cewa ya mutu tun kwanan uku baya kana aka ajiye gawar shi.
Kudin fansa da masu garkuwar suka nema
Bayan sace shi da suka yi, masu garkuwan sun bukaci iyalin dan majalisar da biyan naira miliyan N75 na kudin fansa cikin makon farko na janairu 2018.
kamar yadda majiya suka shaida ma wakilin jaridar Punch, masu garkuwan sun tuntubi wani abokin shi domin karban kudin fansa da suka bukaci a biya su.
source http://ift.tt/2DBgUyp
Post A Comment:
0 comments so far,add yours