Ango Chidimma da amarya Sophy Ijeoma

Kai ga 6 ga wata bayan amincewar iyayen su sai gashi an daura auren su na gargajiya bisa al'adar yan kabilar Ibo.

Wani saurayi ya samu biyan bukata yayin da wata ta amince da bukatar da ya nema na yin aure bayan kwana shidda da duk wanda ta amince dashi.

A ranar 30 ga watan disamba 2017 ne Chidinma  Obodoechina  Amedu ya wallafa bukatarshi a shafin sa na facebook cewa duk macen dake da niyan aurar shi ta bayyana kanta . kuma idan har ta amince za'a daura auren su ranar 6 ga watan farko na 2018.

*Idan kinji haushin rashin aurena ki turo min lambar mahaifin ki - martanin da Maryam Booth ta mayar ma wata da ta nema ta da bakar maganar

 

Abun kamar wasa sai ga dinbim yan mata sun sanar masa da amincewa su da wannan bukatar tashi amma ta Ijeoma Sophy ya tsole masa ido inda ta mayar masa da amsa, cewa zata amince da wannan neman da yake, idan har ya shirya ya tura mata sako ta musamman su kai karshe.

*Tsohon dan majalisar dattawa mai shekaru 87 ya auri sabuwar amarya

 

Bayan kwana biyu da aukuwar haka sai ga Amedu yayi tattaki daga garin Abuja zuwa jihar Enugu inda Sophy take har ya gana da iyayen ta.

Kai ga 6 ga wata bayan amincewar iyayen su sai gashi an daura auren su na gargajiya bisa al'adar yan kabilar Ibo.



source http://www.pulse.ng/hausa/saurayi-ya-auri-budurwa-bayan-kwana-shida-da-haduwa-id7876553.html
Share To:

Anonymous

Post A Comment:

0 comments so far,add yours